1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu

July 16, 2010

Bayan kammala gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya matsalar ƙyamar baƙi ta zama ruwan dare a Afirka ta Kudu

https://p.dw.com/p/ONKH
An kammala gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya a Afirka ta KuduHoto: picture alliance / dpa

A dai ranar lahadi da ta wuce ne aka kammala gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya a Afirka ta Kudu, gasar da bisa ga ra'ayin jaridun Jamus ta haɗa kan Afirka waje ɗaya, amma a halin yanzu tuni murna ta sake komawa ciki, inda aka shiga kai hare-hare kan baƙi baƙar fata daga Zimbabwe da sauran ƙasashen Afirka. A cikin nata rahoton dai jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

Simbabwer fürchten Gewalt in Südafrika Emily aus Simbabwe - Flüchtling in Südafrika.
'Yan ƙasar Zimbabwe na cikin hali na ɗarɗar a Afirka ta KuduHoto: DW/Anna Kuhn-Osius

"Tun makonni da dama da suka wuce ne dai aka fara yayata farfagandar ƙyamar baƙi da fatattakarsu daga Afirka ta Kudu da zarar an kawo ƙarshen gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya. Kimanin 'yan ƙasar Zimbabwe 500 ne suka samu irin wannan saƙo na barazana an kuma fatattaki kimanin 80 daga cikinsu. To sai dai kuma su kansu 'yan ƙasar Afirka ta Kudun ƙaddara kan rutsa da su inda masu kai harin kan yi zaton baƙi ne su kuma kai musu hari, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta nunar."

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta leƙa ne ƙasar Uganda inda tayi sharhi akan harin da aka kai kan wasu masu kallon gasar ƙwallon ƙafar ta cin kofin duniya ta akwatin telebijin a Kampalar Uganda, inda ta ce:

"Kashe-kashe na gilla ne suka biyo bayan gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya a Afirka ta Kudu domin kuwa a daidai lokacin da mutane suka hallara domin kallon gasar ƙarshe kuma ya rage minti biyu kacal domin kammala gasar a ƙarin lokacin da aka yi, bamabamai suka yi bindiga a sassa uku na birnin Kampala, fadar mulkin ƙasar Uganda. A dai babban birnin na Uganda akwai 'yan ƙasar Somaliya masu tarin yawa, waɗanda suka yi ƙaura daga ƙasarsu domin tserewa daga ta'asa da sauran matakai na rashin imani da ƙungiyar Al-Shabab ke ɗauka a ƙasar. Sai dai kuma a tsakanin waɗannan 'yan gudun hijira akwai surkin 'yan Al-Shabab da suka sulale zuwa Ugandan."

Uganda / Anschlag / Kampala
Harin ta'addanci a Kampala, UgandaHoto: AP

Ita ma jaridar Die Tageszeitung ta gabatar da nata sharhin inda take cewar:

"A dai halin da ake ciki yanzu 'yan ƙasar Somaliya dake zaman hijira a Uganda suna cikin wani mawuyacin hali na zaman ɗarɗar saboda su ne suka fi rinjaye a tsakanin mutanen da hare-haren ta'addancin da aka kai a Kampala ranar lahadi da ta wuce ya rutsa da su. Abin takaici game da lamarin kamar yadda 'yan Somaliyan ke gani shi ne za a shafa wa illahirinsu kashin kaza ba za a banbanta tsakanin 'yan ta'adda masu alhakin harin da 'yan Somaliya kimanin dubu 10 da suka nemi mafaka a Kampala don tafiyar da rayuwarsu a cikin lumana da kwanciyar hankali ba."

A wannan makon Faransa ta gudanar da bikin juyin-juya-halinta da ta saba gudanarwa a kowace ranar 14 ga watan yulin kowace shekara. To sai dai kuma a wannan karon Faransar ta gayyaci shuagabanni da sojoji daga Afirka domin halartar wannan biki. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

"Ɗaya daga cikin dalilan wannan gayyatar shi ne kasancewar akasarin ƙasashen Afirka renon Faransa, a wannan shekarar ce suka cika shekaru 50 da samun 'yancin kansu daga Faransar a sakamakon haka ƙasar take fafautukar mayar da lamarin kamar dai wani biki ne nata, kuma hakan ce ta sanya shugaba Nikolas Sarkozy bai halarci wani biki ko da guda ɗaya da wata ƙasa daga cikin ƙasashen na Afirka suka shirya ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita:Yahouza Sadissou Madobi