1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙura ta lafa a zirin Gaza

October 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buhb

A yayin da Palestinu,, ke shirin karɓar baƙuncin sakaratiyar harakokin wajen Amurika,, ƙura ta ɗan laffa a zirin Gaza, inda a ranar jiya aka yi kwashi ba daɗi tsakanin magoyan bayan Hamas da na Fatah , wanda a sakamkon sa, mutane 8 su ka rasa rayuka, da dama su ka ji mummunan raunuka, tare da assara dukiyoyin mai tarin yawa.

Saidai duk da lafawar ƙura da aka samu ,har yanzu jijiyoyin wuya ɓangarorin 2 ,ba su kwanta ba.

Tun bayan da Hamas ta kama ragamar jagorancin ƙasar Palestinu,wannan shine faɗa mafi muni, da ya ɓarke tsakanin ta, da magoya bayan shugaba Mahamud Abbas.

A sakamakon ganawar gaggawa da su ka yi,shugaban hukumar Palestinawa, da Praminista Isma´il Hanniey, sun yi kiran jama´a, su kwantar da hankali, su kuma, fa´inci juna, a cikin wannan wata mai tsarki na Ramadan.

A halin da ake ciki,opisoshin ministoci daban-daban na ƙasar, na rufe, da kuma sauran manyan ma´aikatu.

Ɓarkewar wannan arangama, na da nasaba da rashin biyan albashin ma´aikatan gwamnati, tun watani da dama da su ka gabata.