Ƙungyar al-Qaida a yankin Magreb ta yi iƙirarin kai harin Aljiyas
December 12, 2007Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi tir da tagwayen hare haren bama bamai da aka kai jiya a Aljiyas babban birnin ƙasar Aljeriya yana mai cewa wani hari ne na matsorata. Daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu a hare haren da aka kai da motoci akwai akalla jami´an MƊD 11. Ɗaya daga cikin bama-baman ya fashe ne a gaban wani gini dake kunshe da ofisoshin MƊD sannan daya bam din kuma ya tashi a kusa wata bas dake ɗauke da dalibai. Ma´aikatar cikin gidan Aljeriya ta ce mutane 26 suka rasu amma majiyoyin asibiti na cewa fiye da mutane 60 suka rigamu gidan gaskiya sakamakon fashewar bama-baman. Hukumomin Aljeriya sun ce mutane 177 suka samu raunuka. A cikin shafin ta na intanat ƙungiyar al-Qaida a yankin arewacin Afirka ta yi iƙirarin kai hare haren.