1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar "Welthungerhilfe" ta gabatad da rahonta na shekara-shekara.

YAHAYA AHMEDMay 30, 2006

Ƙungiyar "Welthungerhilfe" na ɗaya daga cikin muhimman ƙungiyoyin ba da taimakon agaji masu zaman kansu a nan Jamus. A cikin rahotonta na shekara-shekara da ta gabatar a wannan makon a birnin Berlin, ƙungiyar ta bayyana irin ayyukan da ta gudanar a ƙasashe daban daban na duniya, waɗanna annoba iri-iri suka shafa.

https://p.dw.com/p/BvTY
Shugaban Ƙungiyar "Welthungerhilfe", Ingeborg Schäuble, lokacin gabatad da rahton.
Shugaban Ƙungiyar "Welthungerhilfe", Ingeborg Schäuble, lokacin gabatad da rahton.Hoto: dpa

Ƙungiyar Welthugerhilfe ta ce kusan kashi ɗaya bisa uku na kuɗaɗen da ta samu a shekarar bara, sun zo mata ne ta hanyar karo-karo daga jama’a. Kashi biyu bisa uku kuma, ta samo su ne daga tallafin da hukumomi kamarsu Hukumar Ciyad da Duniya da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, da gwamnatin tarayyar Jamus da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, wato EU ke bayarwa. Ƙungiyar ta bayyana cewa, ta kashe kuɗaden ne a kan ayyuka ɗari 3 da 31 a cikin ƙasashe 49. Da take gabatad da rahoton ƙungiyar na shekara-shekara a birnin Berlin, shugabanta Ingeborg Schäuble, ta nanata ɓangarorin da ta fi ba da ƙarfi ne wajen gudanad da ayyukanta:-

„A nahiyar Afirka, ɗaya daga cikin yankunan da muka fi ba da karfi, ƙungiyar Welthugerhilfe ta kashe kimanin Euro miliyan ɗari da 10. Mun kuma kashe fiye da Euro miliyan 60 a yankunan Asiya. Sa’annan abin da ya saura kuma, mun yi amfani da su ne a Latinamirka.“

Ƙungiyar ta ce, a nahiyar Afirka dai, ta duƙufad da mafi yawan aikinta ne a yankin Darfur, inda kullum ake ciyad da mutane kimanin miliyan 3 da ɗigo 5. Idan aka sami zaman lafiya, har ’yan gudun hijiran suka sami damar komawa ƙauyukansu, ƙungiyar z ata taimaka musu, wajen sake gina matsugunai da wasu ababan inganta halin rayuwarsu, inji Malama Schäuble. A cikin watan Yulin shekarar bara, ta ce ƙungiyar ta agaza wa mutane fiye da dubu ɗari da 40, waɗanda bala’in yunwar nan ta addaba a ƙasar Nijer. A ƙasar Kongo kuma, jami’an ƙungiyar sun tallafa wajen sake gina hanyoyi da cibiyoyin kiwon lafiya. A ƙasar Mali kuma, sun taimaka wajen gina rumbunan adana abinci, sa’annan suka giggina guraban tara ruwan sama a ƙasar Kenya, don amfani da shi daga baya. A nahiyar Asia kuwa, ƙungiyar ta ce tafi mai da hankalinta ne wajen magance matsalolin da annobar igiyar ruwan nan ta Tsunami ta haddasa:-

„A cikin ƙasashe 4, waɗanda annobar Tsunamin ta fi addaba, wato Sri Lanka, da Indonesiya, da Indiya da Thailand, jami’anmu sun taimaka wa fiye da mutane dubu ɗari 80 masu neman taimako cikin gaggawa. Bayan taimakon agajin da muka bayar, mun kuma tallafa wajen sake gina yankunan da Tsunamin ta ragargaza. A ƙasashen da Tsunamin ta yi ɓarna dai, kawo ƙarshen shekarar bara, mun gina gidaje dubu 3, sa’annan kuma mun gayra ko kuma gina jiragen ruwan masunta dubu 3. Mun sake gina rijiyoyi ɗari 5, sa’annan muka bai wa musan mutane dubu 14 damar komawa harkokinsu na kasuwanci, don su iya ciyad da iyalansu.“

A nan Jamus kawai, kusan Euro miliyan 44 da ɗigo 5 ne jama’a suka ba da gudummowa, don tallafa wa waɗanda Tsunamin ta addaba. Ƙungiyar Welthugerhilfen dai ta kuma tallafa wa ɗimbin yawan jama’ar da girgizar ƙasa ta mai da su marasa galihu a ƙasar Pakistan. Ta kuma gina na’urorin sanad da hukumomi kan ɓarkewar annoba cikin lokaci, kamarsu guguwar iska ko ambaliyar ruwa, a ƙasashen Tajikistan a yankin Asiya, da kuma Nicaragua a Latinamirka.

Ƙungiyar ta Welthungerhilfe dai ta ce mafi yawan kuɗaɗen da take samu, tana amfani da su ne wajen gudanad da ayyukan agaji a sassa daban-daban na duniya. Kashi ɗaya da ɗigo 2 cikin ɗari ne kawai take kashewa kan jami’anta.