1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Tarayyar Afirka na shawarwari da Sudan a kan yankin Darfur.

September 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bujx

Ƙasar Sudan ta nanata cewa, ba za a sami wani giɓi na rashin isassun jami’an tsaro ba, idan dakarun kare zaman lafiya na Ƙungiyar Tarayyar Afirka suka janye daga yankin Darfur a ƙarshen wannan watan. Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Jamal Mohammed Ibrahim ya ce Sudan dai ba ta kori dakaruun daga ƙasar ba. Amma idan aka janye su ma, ba za a huskanci wata matsalar tsaro ba a yankin Darfur. Dakarun kare zaman lafiyar, waɗanda yawansu ya kai dubu 7, sun gaza kare lafiyar jama’a a duk faɗin yankin na Darfur, wanda girmansa ya kai faɗin ƙasar Faransa. Hakan kuwa na da nasaba ne da rashin kuɗaɗe da kuma isassun kayan aiki da soji da rundunar ke huskanta.

A ran juma’ar da ta wuce ne dai babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya yi gargaɗin cewa nauyin duk wani abin da zai auku ga fararen hular yankin Darfur, zai rataya ne a wuyar mahukuntan ƙasar Sudan ɗin, idan bayan janyewar dakarun ƙungiyar Tarayyar Afirka, Khartoum ba ta amince da maye gurbinsu da dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniyar ba.