1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Tamil ta shafe shekaru 33 tana fafutukan kafa ƙasar Tamil

May 27, 2010

An dai kafa wannan ƙungiya ta Tamil Tigers ce a ranar 5 ga watan Mayun shekakar 1976 da nufin kafa wata 'yantacciyar ƙasar 'yan ƙabilar Tamil

https://p.dw.com/p/NYjM
Shugaba Mahinda Rajapaksa na Sri LankaHoto: AP

An dai kafa wannan ƙungiya ta Tamil Tigers ce a ranar 5 ga watan Mayun shekakar 1976 da nufin kafa wata 'yantacciyar ƙasar 'yan ƙabilar Tamil a yankin Arewacin Sri lanka kafin a murƙusheta a watan mayun shekarar 2009. Wato dai ta shafe shekaru 33 tana fafutukan kafa yankin na Tamil a ɗaya daga cikin faɗace-faɗace mafi tsawo a yankin  Asia.

A tsawon wa'yannan shekaru da ƙungiyar ta Tamil ta kwashe tana faɗa da dakarun gwamnatin Sri Lanka ta samu nasarar ƙaddamar da hare-haren ƙunar baƙin wake masu girma akan cibiyoyin gwamnati da dama, kai harma da shugabanin ƙasashen Sri lanka da Indiya da sauran 'yan siyasa masu goyon bayan gwamnatin Sri lanka.

Wasu daga cikin shugabannin da ƙungiyar ta halaka sun haɗa da shugaba Ranasinghe Premadasa na Sri Lanka a 1993 da Firaministan Indiya Rajiv Gandhi a 1991.

Koda yake ƙungiyar na cikin jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ƙasashe da dama basa hulɗa dasu, amma kuma a fili yake cewar, ƙungiyar na samun ƙuɗaɗen gudanar da ita ne daga 'yan ƙabilar ta Tamil dake zaune a ƙasashen ƙetare, irin su nan Turai da Amirka da kuma Indiya.

Tun lokacin da aka kafa ƙungiyar kawo ga lokacin da Sojojin Sri lanka suka murƙushe ta, ƙungiyar na ƙarƙashin jagorancin shugabanta daya kafata ne wato Velupillai Prabhakaran.

Kuma sau da yawa ansha zama teburin samun zaman lafiya da ita ba tare da samun nasara ba.

Bayan samun galaba akan ƙungiyar tare da kashe shugabannnin ta da dama, shugaban Sri Lanka Mahinda Rajapaksa ya aiyana samun nasara akan  Tamil Tigers. Sai dai har yanzu akwai wasu 'yan ƙabilar ta Tamil dake zaune a ƙasashen ƙetare dake cigaba da yaɗa manufofin ƙungiyar a ƙarƙashin wani sabon shugabanta mai suna Visvanathan Rudrakumaran.

Ƙarin bayanai daga Wikepidea

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed