1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Hamas ta yi watsi da sharuɗɗan da ƙasashen Yamma suka shimfiɗa mata.

September 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bujw

Ƙungiyar Hamas, da ke jan ragamar mulkin Hukumar Falasɗinawa a halin yanzu, ta sake yin watsi da sharuuɗɗan da ƙasashen Yamma suke neman ganin ta cika kafin su fara hulɗa da gwamnatin da take jagoranci. A cikin wata fira da ya yi da kamfanin dillancin labaran AFP, kakakin ƙungiyar, Sami Abu Zuhri, ya ce Hamas na duk iyakacin ƙoƙarinta wajen ganin cewa an soke takunkumin da aka sanya wa Hukumar Falasɗinawan. Amma ba za ta nemi cim ma wannan burin ba, idan yin hakan zai cuci al’umman Falasɗinun da kuma taushe musu ’yancinsu.

Tun da Hamas ta lashe zaɓen Falasɗinawa a cikin watan Janairun wannan shekarar ne, ƙasashen Yamma suka katse duk wata hulɗa da Hukumar Falasɗinawan, suka kuma tsai da taimakon da suke ba ta, wanda suka ce ba za su maido da shi ba, sai ƙungiyar ta yi Allah wadai da duk wasu ayyukan tashe-tashen hankulla, ta amince da Isra’ila, sa’annan kuma ta yi amanna da duk wasu yarjejeniyoyin da Isra’ilan da Hukumomin Falasɗinawa na da suka sanya hannu a kansu.

Kakakin ƙungiyar Hamas, Abu Zuhri dai ya ce, ƙungiyar ma na goyon bayan shirin kafa gwamnatin haɗin kai, amma fa wadda Falasɗianawan da kansu suka ƙirƙiro kuma suka kafa, ba wadda ƙasashen ƙetare suka angaza musu ita ba.