1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Haɗin Kan Turai ta ce za ta yi wa Iran wani sabon tayi.

May 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuyO

Ƙasashen Ƙungiyar Haɗin Kan Turai sun ce suna tsara wasu shirye-shirye don yi wa Iran wani sabon tayi mai tsoka, na ba ta tallafi a fannonin cinikayya da tsaro, da burin cim ma shawo kan ƙasar ta dakatad da shirye-shiryenta na mallakar cibiyoyin makamashin nukiliya. Kafin taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar da za a yi yau a birnin Brussels, babban jami’in Ƙungiyar mai kula harkokin ƙetarenta, Javier Solana, ya ce tayin mai fa’ida ne da kuma karimci. Amma ita Iran ɗin da kanta, ta ce za ta yi watsi da duk wani tayin da za a haɗa da wasu sharuɗɗa na ta dakatad da ayyukan sarrafa yureniyum.

A wata sabuwa kuma, wani babban jami’in fadar White House a birnin Washington, ya yi watsi da kiran da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya yi, inda ya bukaci Amirkan da ta shiga shawarwari da Iran kai tsaye a kan wannan batun. Jami’in, Stephen Hadley, wanda kuma shhi ne mai bai wa shugaba Bush shawara a kan harkokin tsaro, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya ce dandalin da ya dace wajen tattauna batun makamashin nukiliyan na Iran.