1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar EU ta yi a game da sakamakon zaɓe a ƙasar Congo

August 9, 2006
https://p.dw.com/p/BunE

Jamiái masu sa ido na ƙungiyar tarayyar turai kan zaɓen ƙasar Congo sun buƙaci gudanar da gaskiya a yayin ƙidayar kuriú a zaɓen ƙasar mai ɗumbin tarihi. Jamián sun yi kashedin cewa baiyana sakamakon da bai kammala ba, na iya haifar da yamutsi a ƙasar. Wani ofishin gunduma na hukumar zaɓe ya kafe sakamakon farko a hukumance na mazaɓu takwas daga cikin mazabu 169. Masu lura da zaɓen sun ce ana fuskantar jan aiki a ƙidayar ƙuriún a wasu yankuna. Tawagar ƙungiyar tarayyar turai sun lura cewa gobarar da ta tashi a wasu ofisoshin zaɓe guda biyu a birnin kinshasa ta kone ƙuriú masu yawan gaske, yayin da wasu jamiái masu sa idanu aka haramta musu shiga cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe. Tawagar ta kara da cewa babu cikakken tsarin tabbatar da gaskiya da daidaito a ƙidayar ƙuriún. A ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata Miliyoyin alúmar ƙasar Congo suka kaɗa ƙuriá a zaɓen shugaban ƙasa dana yan majalisun dokoki a karon farko cikin shekaru 40 a tarihin ƙasar. Jinkiri da ake samu wajen ƙidayar ƙuriún da kuma ruɗanin da suka dabaibaye harkokin zaɓen na haifar da shakku da zargin magudi a zukatan jamaár ƙasar.