1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

031108 EU Kongo

Becker, Michael, Brüssel (MDR)November 4, 2008

Die EU-Außenminister habe sich von einem militärischen Engagament im Krisengebiet Ost-Kongo distanziert. Die EU wolle aber diplomatisch und politisch helfen, den Konflikt beizulegen.

https://p.dw.com/p/Fn6B
´Yan gudun hijira na tserewa rikicin gabashin KongoHoto: AP

Ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai su nesanta kansu daga duk wani shiri na ɗaukar matakan soji a yankin gabashin ƙasar Janhuriyar Demoƙuraɗiyyar Kongo inda ake fama da rikici. To sai dai ministocin sun ce ƙungiyar EU za ta taimaka domin a warware wannan rikici a diplomasiyance.

A daidai lokacin da aka buɗe zaman taron na ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar tarrayyar Turai a birnin Marseille na ƙasar Faransa, ƙungiyar agaji ta Birtaniya wato Oxfam ta yi kira ga ƙungiyar EU da ta aike da dakaru Kongo don taimakawa dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya. Ƙungiyar ta Oxfam ta ce ƙungiyoyin agaji na fama da matuƙar wahala wajen kai kayan agaji ga ´yan gudun hijira. Wani ma´aikacin wata ƙungiyar agaji ta Jamus wato Caritas a garin Goma, ya ce dubun dubatan ´yan gudun hijira a gabashin Kongo na cikin wani bala´i.

To sai dai duk da haka ƙungiyar EU ta ce a yanzu ba ta da niyar ɗaukar wani matakin soji. A ranar Lahadi da ta gabata sakataren harkokin wajen Birtaniya David Miliband da takwaransa na Faransa Bernard Kouchner sun je Kongo don ganewa idonsu halin da ake ciki. Dukkansu biyu sun jadadda cewa an fi nuna buƙatar girke dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya a Kongo, kamar yadda minista harkokin wajen Faransa ya nunar.

Ya ce: "A shirye muke mu taimaka, to amma da farko dole ne mu tantance yadda za a tafiyar da aikin dakarun MƊD tukuna."

Ya ƙara da cewa sojojin MƊD na da isassun kayan aiki da jiragen sama masu saukar ungulu haɗe da yawan sojoji sama da dubu 17, a saboda haka dole sai an bincika an ga yadda za a inganta aikinsu. To sai dai a nasa ɓangaren sakataren harkokin wajen Birtaniya David Miliband cewa yayi.

Ya ce: "Ya zama dole mu yi magana kan yadda dakarun MƊD za su yi aiki da yadda mu kuma za mu taimaka a siyasance da kuma a diplomasiyance. Ba wanda ya yi watsi da ɗaukar matakin soji daga ɓangaren EU, amma an fi buƙatar sojojin MƊD.

Shi kuwa ƙaramin minista a ma´aikatar harkokin wajen Jamus Günter Gloser cewa yayi.

Ya ce: "Abin da muke buƙata yanzu a wannan yanki shi ne maslaha ta siyasa da yadda za a taimakawa tawagar dakarun MƊD da ke a ƙasar ta Kongo."

Wato abin nufi dai a nan shi ne tarayyar Turai za ta taimaka to amma ba a fannin soji ba. A makon da ya gabata ƙasar Faransa dake riƙe da shugabancin EU ta nuna goyon baya ga ɗaukar matakan soji to sai dai ta ce manyan ƙasashen ƙungiyar kamar Jamus na adawa da wannan mataki. A zaɓen da aka yi a Kongo shekaru biyu da suka wuce dakarun EU ne suka tabbatar da tsaro a ƙasar. Tun sannan dai gwamnati a Berlin ba ta sha´awar aikewa da sojoji Afirka musamman a yankuna masu fama da rigingimu.

Ya zuwa yanzu hedkwatar ƙungiyar EU a birnin Brussels ta ware Euro miliyan huɗu ga ´yan gudun hijirar Kongo, kuma ta ce ana iya ƙara yawan wannan taimako.