1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar Al-Shebab ta yi barazanar kai hare hare

July 15, 2010

Shugaban ƙungiyar Al-Shebab na ƙasar Somaliya Mohammed Abdi Godane ya sanar da cewar ƙungiyar za ta kai wasu sabbin hare hare

https://p.dw.com/p/OKo8
Dakarun ƙungiyar' Al-ShebabHoto: AP

Ƙungiyar Al-Shebab ta yi barazanar kai wasu sabbin hare hare, bayan wanda ta kai a ranar Lahadin da ta gabata wanda a cikinsa sama da mutane 70 suka rasa rayukansu.

A cikin wani jawabi da shugaban ƙungiyar Mohammed Abdi Godane ya yi ta gidan rediyon ƙasar ta Somaliya a yau Alhamis ya ce abinda ya faru a Kampala, somin taɓi ne, domin kuwa ya ce nan gaba za su sake kai wasu hare haren.

Wannan hari wanda shi ne na farko da ƙungiyar ta Al-Shebab ta kai a waje, na da yunƙurin yin ramuwar gayya ga ƙasashe maƙobta dake bada gudunmuwar sojoji ga rundunar kiyaye zaman lafiya ta Afirka dake tallafawa halartacciyar gwamnatin ƙasar Somaliya .

Yanzu haka dai ƙasar Burundi ta ƙara ƙarfafa matakan tsaro akan wannan barazana kamar yadda wani babban hapsan sojin ƙasar Manjo janar Godefuwa ya bayyana

"Mun yi rigakafi na matakan da suka dace na tsaro a ƙasar Burundi kuma muna neman goyon bayan al'umma ƙasa da su ba mu haɗin kai domin ba a san ta inda mugu zai shigowa ba."

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal