1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta yi alkawarin bai wa Lebanon taimako don ta sake gina ƙasar.

August 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bum7
Hoto: picture alliance /dpa

Ministocin harkokin wajen Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, sun yi wano taro yau a hedkwatar ƙungiyar da ke birnin al-Ƙahira, inda suka ɗau alkawarin bai wa Lebanon taimako don sake gina ƙasar, bayan ragargaza biranenta da Isra’ila ta yi. Rahotannin da suka iso mana daga birnin al-Ƙahiran sun ce ministocin ƙasashe 17 daga cikin ƙasashe 22 mambobin ƙungiyar ne suka halarci taron, wanda shi ne na farko tun da aka cim ma tsagaita buɗe wuta a makon da ya gabata, a yaƙin da Isra’ila ke yi da mayaƙan ƙungiyar nan ta Hizbullahi. Rahotanni sun ce Siriya, wadda ke goyon bayan ƙungiyar Hizbullahin ba ta tura ministan harkokin wajenta zuwa taron ba.

Sauran ministocin ƙasashen da suka halarci taron, a cikinsu har da na Aljeriya, da Sudan, da Tunisiya, da Yemen da Hukumar Falasɗinawa, sun goyi bayan shawarar shirya wani taron ƙolin ƙasashen Ƙungiyar da Saudiyya ta gabatar, wanda za a gudanar a birnin Makka.

Ministan harkokin wajen Kuwaiti, Sheikh Mohammad al-Salem al-Sabah, ya faɗa wa maneman labarai cewa gwamnatinsa ta ware kuɗi kimanin dola miliyan ɗari 8 don tallafa wa Lebanon sake gina ƙasarta. Ita gwamnatin Lebanon ɗin da kanta dai, ta ce za ta bukaci kimanin dola miliya dubu 3 da ɗari 6 don sake gina kafofinta na fararen hula da Isra’ila ta ragargaza.