1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar ƙasashen larabawa ta bukaci aika tawagar Majalisar Dinkin Dunia a gabas ta tsakiya

November 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bubz

Ƙungiyar ƙasashen larabawa,sunyi kira ga hukumar kare haƙƙoƙin jama´a ta MDD ta ɗauki matakan gaggawa, na aika tawagar bincike a yankin gabas ta tsakiya, domin tantance assararorin da Isra´ila ta hadassa a Palestinu, a sakamakon hare-heran da ta ke ci ga da kaiwa.

Tawagar zata gunadar da bincike, a kan al´ammuran take haƙƙoƙin bani adama, da Isra´ila ke aikatawa, ba tare da dunia ta daga yatsa ba.

Ƙasashen Bahrein, da Pakistan su ka ga gabatar da wannan shawara, wace kuma ta samu goya baya, daga ƙarin ƙasashe 23, daga jimmilar ƙasashe 47, da hukumar ta ƙunsa.

Saisai manazarta al´ammura, na kyauttata zaton wannan haka, ba taza cimma ruwa ba, ta la´akari, da goyan bayan da Isra´ila ke ci gaba da samu daga Amurika.

Ranar asabar ma da ta wuce,Amurika ta hau kejera naƙi, a komitin Sulhu na MDD, a game da batun ɗaukar matakan yin Allah wadai, ga Isra´ila, a sakamakon hare- haren da ta kai Palestinu.