1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

300710 Streubomben Konvention

July 31, 2010

A wannan Lahadin ƙudurin ƙasa da ƙasa da ya haramta amfani da ƙananan bama-bamai dake tarwatsewa bayan harba uwar bam, ke fara aiki.

https://p.dw.com/p/OZ23
Hoto: AP

Dubun dubatan fararen hula ne suka halaka sakamakon waɗannan ƙananan bama-bamai dake fashewa daga bisani. Saboda ƙanƙantarsu da kuma rashin fashewa nan-take idan an harba su, waɗannan bama-bamai kan faɗa hannun yara suna yi musu mummunar illa da suke shafe tsawon rayuwarsu suna jinya.

Ƙasashe sama da 100 suka sanya hannu kan ƙudurin na haramta amfani da ƙananan bama-bamai yayin da kimanin 40 ciki har da Jamus suka rattaɓa masa hannu. Bayan sanya masa hannu a birnin Oslo, an kwashe watanni 20 kafin ƙudurin ya fara aiki a wannan Lahadin. Paul Vermeulen daraktan ƙungiyar naƙasassu ta duniya wato Handicap International ya nuna farin cikinsa game da wannan ci-gaba da aka samu.

"Karo na biyu tun bayan ƙudurin haramta nakiyoyin ƙarƙashin ƙasa, ƙasashen duniya sun matsa ƙaimi don ganin an haramta wani makami da ake yawaita amfani da shi."

Da wannan ƙudurin ƙasashen duniya sun haramta amfani da ƙerawa da samarwa da jibgewa da kuma yaɗuwar ƙananan bama-baman. Su dai irin waɗannan bama-baman ana saka su ne cikin wasu tukane da jiragen sama ke jefowa, bayan sun taɓa ƙasa tukanen kan buɗe su watsa ɗaruruwan bama-baman. Kawo yanzu an yi amfani da irin waɗannan makamai a kasashe sama da 20, musamman ma a ƙasar Vietnam inda aka jefa bama-baman fiye da dubu 400 a lokacin yaƙin ƙasar.

Streubomben Libanon
Ƙananan bama-bamai a tsakanin duwatsu. Suna iya yin bindiga da zarar wani abu ya taɓa suHoto: Organisation mag/MA Group Lebanon

To sai dai a lokuta da dama ƙananan bama-baman ba sa fashewa nan-take su kan maƙale akan bishiyoyi ko su faɗi a wuraren wasan yara waɗanda ke ɗaukar makaman a matsayin kayan wasa. Bisa ƙiyasin ƙungiyar Handicap International kusan kashi 98 cikin 100 na waɗanda suka raunata sakamakon fashewar ƙananan bama-baman fararen hula ne. Bisa wannan ƙudurin yanzu ƙasashe sun yi alƙawarin ba da taimakon kiwon lafiya da na kwantar da hankulan waɗanda bama-baman suka yiwa lahani. Florian Westfal na ƙungiyar agaji ta Red Cross ya bayyana wannan matakin da cewa gagarumin aiki ne da za a ɗauki lokaci mai tsawo ana aiwatarwa.

"Duk wanda ƙananan bama-bamai ko nakiyoyin ƙarƙashin ƙasa suka yiwa lahani zai shafe tsawon rayuwarsa yana jinya. Wannan kuwa ya fi shafan ƙananan yara a ƙasashe kamar Libanon da Afganistan. Amma kawo yanzu ba a ɗauki wani matakin daidaita wannan batu ko magance shi ba. Waɗannan mutane na neman taimako duk tsawon rayuwarsu."

Ƙudurin ya tilastawa ƙasashe da su lalata rumbunan adana ƙananan bama-baman a cikin shekaru takwas masu zuwa. Yanzu haka dai wasu ƙasashe kamar Spain da Austriya sun cike wannan ƙa'idar yayin da Jamus za ta kammala lalata dukkan ƙananan bama-bamanta kafin shekara ta 2015. To sai dai kamar yarjejeniyar Ottawa da ta haramta amfani da nakiyoyin ƙarƙashin ƙasa, a wannan karon ma manyan daulolin duniya mafiya ƙarfin soji kamar Amirka, Rasha da China ba su sanya hannu kan yarjejeniyar haramta ƙananan bama-baman ta birnin Oslo ba.

Mawallafa: Pascal Lechler/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar