1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙokarin Jamus na tallafawa ƙasashe masu raunin tattali

May 21, 2010

Mahawarar majalisar wakilai na Jamus dangane bayarda kudaden ceto

https://p.dw.com/p/NU39
Hoto: AP

Majalisar wakilai na Tarayyar  na tattaunawa a birnin Berlin, a dangane da ko  Jamus zata bayar da gudummowar euro miliyan dubu 750, domin ceto ƙasashen da ke da raunin tattalin arziki, kana ke cikin gungun ƙasashe da ke amfani da takardar kuɗin euro. Idan 'yan majalisar suka amince, Jamus zata iya bayar da gudummowar  kusan euro miliyan dubu 150. Wannan dai batu ne daya kasance mai sarkakkiyar gaske a majalisar wakilan na Jamus, sai dai bisa dukkan alamu za a cimma amincewa da shi.

A yanzu haka dai  ministocin harkokin kuɗi na turai dake  taro yau a Brussels, sun mayar da hankalinsu kan mahawarar ta Berlin. Ana saran ministocin kuɗin zasu tattauna kan matsalolin bashin da ke addabar wasu ƙasashen dake amfani da takardun kuɗin na Euro.

Mawallafiya:Zainab Mohammed Edita Yahouza Sadissou