1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080310 Nahost Biden

March 8, 2010

Joe Biden na Amurka ya fara ziyarar aiki a yankin gabas ta tsakiya, adaidai lokacin da ake shirin fara tattaunawar bayan fage

https://p.dw.com/p/MNUF
Joe BidenHoto: picture-alliance/ dpa

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya fara rangadin aiki aiki a yankin gabas ta tsakiya, tare da tabbatarwa da Izraela cewar Washington zata bada hadin kai domin kare duk wata barazana da ka iya fitowa daga ɓangaren Iran.

Biden dake zama mafi girman Jami'in gwamnatin Amurka na farko daya kai ziyara Izraela tun bayan hawan Barack Obama karagar mulki a shekara ta 2009 dai, ana saran zai shawarci mai masaukinsa Izraelan da kada ta gaggauta kai wa Iran hari, adaidai lokacin da shugabannin ƙasashen Duniya ke nazarin kakaba mata sabbin takunkumi.

Ziyarar tasa dai nada ɓangaren kokarin da Amurka keyi na ganin cewar an koma teburin tattaunawa tsakanin Izraela da Palaitinu, bayan dakatar dashi na tsawon watanni 14.

Herr Saeb Oraikat Chief Palestinian Negociator
Saeb ErekatHoto: DW/Samar Karam

 A  ranar lahadin nan ne dai ƙungiyar fafutukar nemarwa Palastinu 'yantacciyyar ƙasa ta PLO ta amince da fara tattaunawar bayan fage tsakanin ɓangarorin biyu. Sai dai bayan da ƙungiyar Palastinawan ta yi amannan fara tattaunwara ta bayan fage,  Gwamnatin  Izraela ta bada umurnin gina sabbin gidaje kimanin 112 a gaɓar yamma da kogin Jordan, batu daya tunzura Palastinawa.

A yayin ziyarar ta Biden dai ana saran zai sanar da lokacin fara tattaunawar bayan fage tsakanin ɓangarorin biyu, a karkashin mai shiga tsakanin wakilin Amurka George Mitchell wanda ya yi tattaunawar karshe da magabatan Jerusalem da  Ramallah.

Saeb Erakat shine mai wakiltar Palastinawa a tattaunawar..

" Kada dukannin gwamnatocin suyi wasa da wannan damar, domin yin watsi da damar zai sake mayar da yankin wani mawuyacin yanayi. Kana cigaban gine-gine da Izraela takeyi a yankin Palastinawa bazai haifar da komai ba, face cigaba da fuskantar rigingimu da tashe-tashen hankula akai akai"

Bayan ganawarsa da Wakilin Amurkan George Mitchel a birnin Kudus Priminista Benjamin Netanyawu ya yi fatan kaddamar da tattaunwar bayan fagen, idan hakan zai jagoranci zama kan teburi domin tattaunawa kai tsaye....

Israel / Benjamin Netanjahu
Benjamin NetanyahuHoto: AP

"Mun sha faɗin cewar, bamu da wani takamammen tsari. Idan ya zamanto wajibi a fara tattaunawa, to Izraela a shirye take. Sanin kowa ne cewar ƙasarmu na muradin fara tattaunawar sulhu, amma san kuma shaidar a yau cewar, za kuma mu iya dakatar dashi"

A yanzu haka dai ɓangarorin biyu sun shirya fara wannan tattaunwar, duk kuwa dacewar na ciki na ciki adangane da dalilan da suka jagoranci rushewar tattaunawar kai tsaye a karshen shekarata 2008, gabannin zaben Izraela.

Mai shiga tsakani a bangaren Palastinu Saeb Erakat ya yi imanin cewar Izraela bazata taɓa amince da bawa palastinawa abunda suke suke muradi ba, wanda shine mallakar 'yantacciyar ƙasa wadda zata hada gaɓar yamma da kogin Jordan da Zirin Gaza.

Mawallafiyya: Zainab Mohammed Edita: Mohammad Nasur Awal