1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin kare Iran daga sabbin takunkumi na ƙasashen Turai

May 16, 2010

Shugabannin ƙasashen Brazil da Turkiyya na Tehran domin tattauna yiwuwar warware matsalar nukiyar Iran

https://p.dw.com/p/NPUH
Mahmud AhamadinejadHoto: AP

Priministan Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na fara wata ziyara yau a birnin Tehran, inda zai haɗe da shugaban ƙasar Brazil Luiz Lula da Silva, akokarinsu na shawo kan Iran wajen amincewa da tayin musayar shirin Nulikiyarta da Mai. Iran ɗin dai ta hakikance cewar shirin Nukiliyarta na samarda makamashi ne amma ba makamai ba, sai dai ƙasasashen yammaci na tsoron haka, inda suka yi wa Iran ɗin tayin bunkasa sinadran uranium ɗin ta a ƙasashen Rasha da Faransa. Amurka da Rasha dai na ganin cewar, tattaunar ta Tehran ita ce dama ta ƙarshen da Iran ke da ita na kaucewa sabbin takunkumin Majalisar Ɗunkin Duniya. A yanzu haka dai Jamus da ƙasashe biyar dake da zaunanniyar kujera a komitin sulhu, na tattauna sabbin takunkumi akan Iran. Brazil dake zama ɗaya daga cikin wakilan komitin 15, taki amincewa da sabbin takunkumin,amadadin haka ta shiga diplomasiyyar warware matsalar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Ahmad Tijani Lawal