1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin daidaita kasuwar ƙwadago a Nahiyar Turai

Ibrahim SaniDecember 6, 2007
https://p.dw.com/p/CYMo

Ministocin sharia da kuma na cikin gida na ƙungiyyar Tarayyar Turai na gudanar da taro, a birnin Brussels na ƙasar Belgium. Jami´an ƙungiyyar na Eu za su tattauna matsaloli ne na shigi da fi ci. Akowace shekara dai an kiyasta cewa, baƙi miliyan biyu ne ke shigowa izuwa mambobin ƙasashen na Eu. Da yawa dai daga cikin ire iren waɗannan baƙi na, a matsayin wata kafa ce ta cike giɓin da ƙasashen ke fuskanta ne dangane da ma´aikata. Ana sa ran wannan taro zai duba yiwuwar dai-dai-ta harkoki na ƙwadago, a tsakanin mambobin ƙasashen. Ɗaya daga cikin hanyoyin sun haɗar da samar da takardar izinin aiki na biyan ´Yan ƙwadago hakkokinsu yadda yakamata. A hannu ɗaya kuma da hukunta duk wani kamfani daya take hakkokin ´Yan kwadagon da su ka fito daga mambobin ƙasashen na Eu.