1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙhaddafi, Mubarack da Buteflika sun hadu a birnin Tripolie

January 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuTW

A ranar jiya talata, an gudanar da taron ƙoli da ya haɗa shugaban Muhammar Ƙhaddaffi na Libya, da takwarorin sa, Hosni Mubarak na Masar, da kuma Abdel Aziz Buteflika na Algeria.

Shugabanin 3, sun tantanna a kann batutuwa da su ka shafi ƙasashen larabawa, mussamman yankin gabas ta tsakiya, Somalia da Sudan, batutuwan da za su mamaye ajendar taron ƙungiyar gamayar Afrika da za a shirya a mako mai zuwa a ƙasar Ethiopia

Hosni Mubarak, yayi anfani da wannan dama, inda yayi masu bayyanin sakamakon ganawar da yayi da sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, a makon da ya gabata.