1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙawance a tsakanin Amirka da Koriya Ta Kudu

December 1, 2010

Amirka da Koriya Ta Kudu za su kammala atisayen soji wanda ke da nufin yin gargaɗi ga Koriya Ta Arewa

https://p.dw.com/p/QMUN
Daya daga cikin jiragen ruwan yakin da Amirka ta yi amfani da su wajen atisayen sojin hadin gwiwa da Koriya Ta KuduHoto: AP

A yau Laraba ce ƙasashen Amirka da Koriya Ta Kudu ke shirye shiryen kawo ƙarshen atisayen soji na haɗin gwiwar da suka yi tsawon kwanaki huɗu suna gudanarwa, sai da kuma har yanzu ana ci gaba da samun zaman ɗar ɗar tare da Koriya Ta Arewa. Atisayen sojin, wanda shi ne irin sa mafi girma a tsakanin Koriya da Kudu da ƙasar Amirka, ya ƙunshi jiragen yaƙi masu saukar ungulu da kuma manyan jiragen ruwan yaƙi, wanda kuma ya zo jim kaɗan bayan da Koriya Ta Arewa ta harba makaman roka a kudancin Koriya Ta Kudu, makaman da kuma suka yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu. Dukkan sassan biyu dai sun yi gargaɗin ƙara matsa ƙaimi a yankin nan gaba. Ita kuwa ƙasar Koriya Ta Arewa cewa ta yi atisayen sojin daya gudana a tekun yankin, wata manuniya ce game da cewar Koriyoyin biyu na dab da faɗawa cikin yaƙi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadissou Madobi