1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Kuba za ta saki firsinonin siyasa

July 8, 2010

Shirin ƙasar Kuba na sakin firsinonin siyasa.

https://p.dw.com/p/ODns
Jaime Ortega da Miguel Angel Moratinos yayin ganawar da suka yi a birnin Havana.Hoto: ap

Cocin Katolika ta ce ƙasar Kuba ta yarda ta saki firsinonin siyasa 52 tare da basu damar ficewa daga ƙasar. Ministan harkokin wajen Spain, Miguel Angel Moratinos ya ce gwamnantin Kuba ta tsai da shawarar yin hakan ne domin buɗe wani sabon babi a ƙasar mai bin tsarin kwaminisanci. A wata ganawa da aka yi tsakanin Shugaba Castro da babban limamin Katolila na birnin Havana, Cardinal Jaime Ortega da kuma Moratinos ne aka ba da sanarwar sakin firsinonin su 52 daga cikin tsegeru 75 da aka cafke aka kuma yanke wa hukuncin ɗauri na watanni shida zuwa shekaru 28 a gidan yari a shekarar 2003.Yin hakan dai na zaman gagarumin matakin sakin tsegeru da tsibirin ya ɗauka bayan shekaru aro aro.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu