1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙasar Jamus ta yaba da ci-gaban da aka samu a yankin Gaza

June 25, 2010

Ministan harkokin waje na ƙasar Jamus Guido Westerwelle ya sheda cewa ana kan hanyar cimma shirin zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/O3gw
Guido WesterwelleHoto: AP

Jagoran diflomasiya na ƙasar Jamus Guido Westerwelle ya yaba da canji matsayin da aka samu na ƙasar isra'ila akan yanki Gaza, bayan da gwamnatin ƙasar ta gabatar da goron gayata ga wata tawaga ta ministocin ƙungiyar Tarayya Turai domin ta kai ziyara gani da ido a yankin don lura da irin ci gaban da aka samu na walwalar jama'aa.

Mista Westerwelle da ya bayyana haka a birnin Bukarest na ƙasar Romaniya inda yake ziyara ya sheda cewa wannan yunƙuri wani mataki ne na farko ga cimma shirin zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Hukumomin ƙasar ta Isara'ila dai sun gayaci ministan harakokin waje na ƙasar Italiya Mista Franco Frattini da ya jagoranci tawagar ta jam'ian diflomasiya na ƙungiyar zuwa yankin Gaza .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umar Aliyu