1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙaruwar waɗanda suka mutu a harin Abuja

October 2, 2010

Gwamnatin Najeriya tace yanzu a hukumance mutane 12 suka mutu bayan harin da gwamnatin ƙasar tace na ta'addanci ne, wanda aka kai jiya a Abuja

https://p.dw.com/p/PSyS
Inda aka kai hari bam a AbujaHoto: AP

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya fito a fili ya kira 'yan fafitikar 'yantar da yankin da ya fito na Naija Delta a matsayin 'yan ta'adda, shugaba Jonathan ya ce 'yan ƙungiyar ta MEND da su ka amsa cewa su suka kai harin bam a dai dai lokacin da ya ke tare da man'yan baƙin duniya da suka zo taya Najeriya murnar cika shekaru 50 da samun ´yancin kai, babu sunan da za'a kira illah 'yan ta'adda. Jonathan ya yi jawabin na sa ne a yau, yayin da wanda su ka mutu sanadiyar harin na jiya su ka ƙaru izuwa mutum 12. Kakakin 'yan sandan Najeriya Jimoh Moshood, ya shaidawa manema labarai cewa mutum sha biyu sun rasu, sakamakon raunukan da su ka samu a jiya. Shi ma kansa shugaban Najeriya Gooluck Jonathan ya ziyarci waɗanda harin ta'addanci ya shafa da ke kwance a asibitin ƙasa na Abuja.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi