1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen ziyara shugaban AU a Cote d`Ivoire

September 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bujk

Shugaban ƙungiyar tarayya Afrika, Denis Sassu Nguesso, ya kammala ziyara aikin da ya kai ƙasar Cote d´ivoire.

A cikin kwanaki 2, ya tantana da shugaba Lauran Bagbo, da Praminista Charles Konnan Banny.

Kalika, Sassou Nguesso, ya gana da shugabanin jami´yun adawa wato, Alassane Watara da Henri Konnan Bedie, da kuma madugun yan tawaye ƙasar, Guillaume Sorro.

Saidai tantanawar ba cimma wani abun zo a gani ba, ta fannin kusanto ra´ayoyin ɓangarorin 2, da ke gaba da juna.

A taron manema labarai da ya kira, shugaban AU, ya nuna takaici, a game da tafiyar hawainiya da ake fuskanta, a yunƙurin warware rikicin siyasar Cote D´Ivoire.

A watan oktoba mai zuwa, a ka shirya gudanar da zaɓuka daban-daban a wannan ƙasa, to saidai hakan ba zai samu ba, ta la´akari da ƙiƙi-ƙaƙar da a ke fuskanta.

Ranar 20 ga watan da mu ke ciki, Majalisar Ɗinkin Dunia zata zaman taro na musamman, a game da makomar siyasar Cote D´Ivoire.