1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen taron shugabanin ƙasashen EU

Hasselbach, Christoph (DW Brüssel)October 17, 2008
https://p.dw.com/p/Fbja
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, a dama tare da shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso yayin taron EU a Brussels.Hoto: AP

Shugabanin na tarayyar Tuari sun koma gida cikin kwanciyar hankali bayan da aka sami haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin su wajen cimma matsaya guda ta samun bakin zaren warware matsalar da ta addabi harkokin hada- hadar kuɗaɗe a duniya baki ɗaya. Sai dai kuma an ɗan sami ƙorafe - ƙorafe a tsakanin shugabanin a game da ƙudirin sauyin yanayin muhalli da kuma batun maida hulɗar dangantaka da ƙasar Rasha. Tun da farko shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy wanda ƙasar sa ke riƙe da shugabancin karɓa -karɓa na ƙungiyar tarayyar Turan ya baiyana cewa wannan wata babbar dama ce wadda bai kamata a yi wasa da ita ba, na yin garanbawul a harkokin hada hadar kuɗaɗen a wannan ƙarni na 21. Yace a dangane da haka a ranar Asabar mai zuwa tawagar tarayyar Turai zata tattauna da shugaban Amirka George W Bush domin yiwa tubkar hanci.

Ɗaukacin ƙasashe 27 na tarayyar Turan sun bada cikakken goyon bayan su ga jadawalin da ƙasashe goma sha biyar na ƙungiyar masu amfani da kuɗin Euro suka gabatar ceto Bankunan daga durƙushewa. Sai dai kuma a waje guda ƙasashen na tarayyar Turai sun buƙaci yin gyara ga harkokin hukumomin kuɗaɗe na duniya domin kaucewa sake faɗawa ciki irin wannan matsalar a nan gaba.


Shugaba Sarkozy na buƙatar saduwa da Bush gabanin babban taron ƙasa da ƙasa wanda zai ƙunshi manyan ƙasashe masu cigaban masanaántu da wasu ƙasashen masu tasowa ta fuskar masanaántun waɗanda suka hada da ƙasashen China da India da zai gudana a watan Nuwamba mai zuwa.


Sai dai kuma a inda taƙaddamar take ita ce kan batun rage hayakin maanántu mai gurbata yanayi. A shekarar da ta gabata, shugabanin tarayyar Turan suka yi alƙawarin rage hayakin masanaántu da suke fitarwa da kimanin kashi ashirin cikin ɗari nan da shekara ta 2020, tare kuma da alƙawarin samar da sabbin dabarun makamashi mara gurbata yanayi.


A waje guda dai wasu daga cikin ƙasashen tarayyar Turan sun fara kokawa da irin tasirin da matakin rage hayakin masanaántu zai haifar ga cigaban ayyukan kamfanonin su, bisa laákari da matsalar hada hadar kuɗaɗe dake neman jefa duniya cikin matsanancin halin tattalin arziki.


Da farko dai ƙasashen Poland da Italiya sun yi barazanar hawa kujerar naƙi, na ƙin amincewa da aiwatar da ƙudirin, to amma shugaba Sarkozy ya ci gaba da nanata buƙatar ƙungiyar ta EU ta martaba alƙawarin da ta ɗauka a saboda haka ya bada shawarar tattauna batun a taron da zasu yi nan gaba a watan Disamba. Yana mai cewa batun muhallin yana matuƙar muhimmancin gaske, da ba zai yiwu a jingine shi saboda matsalar hada hadar kuɗaɗe ba.


Batun maida dangantaka tsakanin ƙungiyar tarayyar Turan da Rasha ya haifar da tada jijiyar wuya a tsakanin wasu shugabani waɗanda ke ganin cewa lokaci bai yi ba da zasu maida hulɗa da ƙasar ta Rasha. A watan satumban da ya gabata ne ƙungiyar tarayyar Turai ta dakatar da dukkan wata tattaunawa da Rasha kan tafarkin hulɗar ƙawance tsakanin ɓangarorin biyu sakamakon faɗan aka gwabza tsakanin Rasha da Georgia wanda ya harzuƙa ƙasashen tarayyar Turan. Ƙasashen Britaniya da Poland da jamhuriyar Czech da Denmark da Lithuania da kuma Sweden na masu raáyin cewa idan aka maida hulɗa da Rasha a yanzu tamkar Rashan ta yi galaba kenan akan su a saboda suka ce kamata yayi a jinkirta tukunna. A yanzu dai ɗage tattaunawa akan Rashan ya zuwa taro na gaba da ƙungiyar tarayyar Turan zata yi a Faransa a ranar 14 ga watan Nuwamba.