Ƙarshen taron G 8 a Saint-Petesbourg
July 17, 2006Yaƙi tsakanin Isra´ila da Hezbollah, na daga batutuwan da su ka mamaye taron ƙungiyar G8, da ya haɗa shugabanin ƙasashe 8 mafi ƙarfi tattalin arziki a dunia.
A tantanwar da su ka yi yau, shugabanin, sun bayyana wajicbin tura rundunar shiga tsakani a kudancin Labanon.
Saidai, duk da yarjejeniyar da su ka rataba hannu a kai jiya, a game da da wannan yaƙi, ƙasashen G8, na fuskantar rarrabuwar kanu.
Shugaban ƙasar France Jaques Chirac, ƙarrara ya nuna adawa da matsayin Amurika, na ɗora lefin ɓarkewar yaƙin a kan ƙungiyar Hezbollah kaɗai.
Saidai baki ɗaya sun bukaci ɓangarorin su ajje makamai, sanan Hezbollah ta yi belin sojojin Isra´ila da ta ke garkuwa da su.
A wani baben kuma, taron Saint Petesbourg, ya tanttana a kan matsalolin tattalin arzikin ƙasashen Afrika.
A dangane da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran, ƙasashen G8, sun yi kira ga hukumomin Teheran, su amince da tayin da, ƙasashe EU, Amurika, Rasha da China su ka yi masu a watan da ya gabata.
A danagane da badakkalar makamami maus lizzami da Korea ta Arewa ta harba akmakonda ya gabata, Rasha da China sun bayana yiwuwar warware rikicin ta hanyoyin diplomatia.