1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarin sojoji 4 na Amurika sun rasa rayuka a Irak.

July 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuFy

A cigaba da rikicin Iraki, wasu Ƙƙarin sojojin Amurika 4 sun sheƙa lahira, tare da masu yi masu passara, yan ƙasar ta Irak.

Wannan al´amari ya abku, a sakamakon tarwatsewar wata bam, gap ga wucewar tawagar sojojin a birnin Bagadaza.

Sanarwar rundunar Amurika, a Irak ta ce duk da wannan saban hari, sojojin Amurika, ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, a yunƙurin su na tsarkake ƙasar Irak daga ayyukan yan ta´ada.

Wannan sune cikamakon sojojin Amurika na 3.625,wanda a hukunce, a ka bayyanar mutuwar su , a filin dagar Iraki, daga farkon mamayar ƙasar, a watan maris na shekara ta 2003 zuwa yanzu.