1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarin haɗin kai da taimakon juna tsakanin EU da NATO

April 26, 2010

Ministocin harkokin waje na ƙungiyar EU sun jaddada buƙatar ƙarin haɗin kai da NATO

https://p.dw.com/p/N7Dl
Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle.Hoto: AP

Bisa ga dukkan alamu dai za'a sami ƙarin haɗin kai da fahimta da taimakon juna a tsakanin kasashen Turai. Hakan ya ƙara baiyana ne a ƙarshen taron da Ministocin harkokin waje na tarayyar turan tare da tawarorinsu na tsaro suka gudanar a Luxemburg inda kuma suka taɓo batun halin da ake ciki a ƙasar Girka.

Ko da yake batun ƙasar Girka baya daga cikin jadawalin taron Ministocin harkokin wajen, kungiyar tarayyar turai dai na taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa ƙasar ta Girka samun mafita daga dumbin matsalolin kuɗaɗe da suka yi mata dabaibayi. Sai dai a cewar Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle babu wani hanzari ga wannan al'amari.

" Idan aka yi hanzarin samar da kuɗi ga ƙasar ta Girka, to kuwa ba za ta tsaya ta yi abin da ya wajaba a gare ta na cusa ɗa'a a harkokinta na kuɗi ba da kuma ƙarfafa waɗannan matakai ba. Saboda haka wajibi ne Girka ta daidaita al'amuran ta. Ba zai yiwu mu ɗauki kuɗaɗen haraji na jama'a domin biyan buƙatun abin da wata ƙasa ta yi da ganganci ba".

Frankreich EU Parlament in Straßburg Jose Manuel Barroso
Shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel BarrosoHoto: AP

Shugaban hukumar tarayyar turan Jose Manuel Barroso da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy sun yi kira a Paris domin bada ɗaukin gaggawa ga ƙasar Girka. Sai a taron na Luxenburg, Ministan harkokin wajen ƙasar Italiya Franco Fratini ya baiyana damuwa a game da kafewar da Jamus ta yi ba ta son ta sauya matsayinta.

Fratini ya kuma yi tsokaci a game da batun sabon sashen da ake so a kafa wanda zai lura da harkokin diplomasiyyar tarayyar turai. Catherine Ashton Jami'ar manufofin ƙetare ta ƙungiyar EU na buƙatar samun amincewar ƙungiyar domin kafa wannan sashe. A dangane da wannan Fratini ya yi bayani yana mai cewa " A yau ba na cikin yanayin da zai iya bada wani haske game da shawarwarin da aka bayar na kafa wannan sashen hulɗar diplomasiyya, saboda kuwa ba ni da wasu cikakkun bayanai kamar tsarin dokokin maáikata da tsarin shugabanci, misali wanene ke da alhakin gudanar da wani aiki. A dukkan waɗannan matakai sai mun hanzarta ɗaukar shawarwari.

Shi kuwa takwaransa na ƙasar Sweden Carl Bildt tuni ya fusata da nawar da ake yi wajen zartar da shawarwari a cikin ƙungiyar ta EU." Ina ganin zai ɗauki tsawon lokaci domin akwai al'amura da dama da ke faruwa a duniya, akwai batun shirin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya wanda ya ƙi gaba ya ƙi ba, ga halin da ake ciki a Afghanistan mai matuƙar damuwa, ga batun Sudan da shi ma ya kamata a duba saboda haka ana ɓata lokaci kuma hakan bai dace ba".

EU Luxemburg Außenminister Treffen NATO-Generalsekretär Anders Fogh Rasmussen
Sakatare Janar na ƙungiyar NATO Anders Fogh RasmussenHoto: AP

A waje guda kuma a na su ɓangaren Ministocin tsaro na ƙungiyar tarayyar turan na buƙatar ƙarin haɗin kai tsakanin ƙungiyar EU da ƙungiyar tsaro ta NATO domin aiki tare. To amma cikin EU ɗin kanta kowace ƙasa na ganin ta isa a cewar Alexander Weis shugaban hukumar tsaro ta ƙungiyar tarayyar turai. Weis ya yi kiran gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a tsakanin ƙungiyoyin biyu, misali kamar amfani da jiragen yaƙi waɗanda ke sarrafa kansu ba tare da matuƙi ba wanda aka fi sani da drones a turance.

" Yace shekaru 25 da suka wuce, wasu ƙasashe shidda na tarayyar turai suka ƙaddamar da shirin bunƙasa jiragen yaƙi guda uku, ka ga za'a iya yin tsimin kuɗi idan da a ce ana da tsari guda na bai ɗaya dangane da jiragen yaƙi a nahiyar turai, to amma yau gashi mun koma kan irin wannan yanayi inda ake muhawara game da samar da wani sashe na diplomasiyya na ƙungiyar tarayyar turai. Muna ganin lokaci ya yi da za mu yi tunanin tafarki guda na tarayyar turai. Wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci ga nahiyar.

Weis ya gabatarwa ministocin wata muƙalla da aka tafka muhawara akanta wadda a ƙarshe ya fuskanci matsananciyar turjiya daga ministocin.

Mawallafa : Christoph Hasselbach /Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru ALiyu