1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarin farashin man fetur a Nigeria

May 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuKd

Gwamnatin tarayyar Nigeria ba zato ba tsammani ta yi ƙarin farashin man fetur da dangogin sa da kimanin kashi goma sha biyar cikin dari. A yanzu man ya tashi izuwa Naira 75 a kowace lita guda. Matakin ya zo kwanaki uku kacal kafin shugaba Olusegun Obasanjo ya sauka daga karagar mulki. Ƙarin farashin wanda ya fara aiki a ranar lahadin nan a dukkanin gidajen mai ba tare da sanarwa ba, ka iya haifar da matsaloli ga sabuwar gwamnatin Umaru Musa Yar Aduá wadda zata karɓi ragamar mulki a ranar Talata mai zuwa. Dama dai tuni Yar Aduán ke fuskantar matsalar rashin amincewa dangane da sakamakon zaɓen da ya baiyana shi a matsayin wanda yayi nasara. A can baya ƙarin farashin man ya haifar da yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago a faɗin ƙasar baki ɗaya. Nigeriar wadda ke zama babbar ƙasa mai arzikin mai a nahiyar Afrika ta dogara ne ga sayo man daga ƙetare kasancewar dukkanin matatun ta basa aiki.