1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarfafuwar dangantaka tsakanin Jamus da Turkiya

October 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuhD

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta buƙaci ƙarfafa danganta ta fuskar aládu tare da musayar raáyi ta fannin addini tsakanin Jamus da Turkiya. Merkel ta baiyana hakan ne a birnin istanbul yayin da take ganawa da P/M Turkiyan Tayip Erdogan. Tun da farko a birnin Ankara, Merkel ta ce ƙudirin Turkiya na shiga ƙungiyar tarayyar Turai, zai dogara ne ga yadda ta cika sharuɗan ƙungiyar da kuma buɗe tashoshin ta na ruwa da filayen jiragen sama ga kayayyakin da ake sarrafawa na ƙasar Cyprus. Shugabar gwamnatin Angela Merkel na tare da rakiyar yan kasuwar ƙasar Jamus. Tuni ta kammala ziyarar tare da taruka da shugabannin yan kasuwa dana addini.