Ƙarfafa haɗin kan tsaro da al´adu tsakanin Nijeriya da Nijer
December 11, 2008Talla
A ci gaba da ƙoƙarin samo ƙwararan hanyoyin ƙarfafa tsaro da zumunci da kyautata al´adu a tsakanin Janhuriyar Nijer da Tarayyar Nijeriya, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Mai Yasin ya naɗa jakadan ƙasar Nijer a Nijeriya Alhaji Ibrahim Musa a matsayin garkuwan masarautun jahohi 17 na gabacin Nijeriya domin ya riƙa haɗa kan sarakuna ƙasashen biyu kan harkokin da suka shafi tsaro da walwalar jama a. Wannan matakin ya samu amincewar ministan tsaro na Nijer. Ana fata wannan sarautar ta garkuwan za ta ƙara zama wata kafar ƙara samun tsaro a tsakanin Nijer da Nijeriya tare da yawaitar arziki da fahimtar juna tsakanin al´umomin ƙasashen biyu.