1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙalubalen zaman lafiya a Dafur

November 15, 2007
https://p.dw.com/p/CE6o

Shugaban sashen kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar ɗinkin duniya Jean Marie Guehenno ya yi kashedin cewa aikin rundunar haɗin gwiwa na Afirka da majalisar ɗinkin duniya don kiyaye zaman lafiya a Dafur ka iya cin tura idan har ƙasashe basu bada gudunmawar da ake buƙata ba na motoci da kuma jiragen sama masu saukar ungulu. Jamiín na Majalisar ɗinkin duniya ya kuma ja hankali a game da rashin cimma yarjejeniya daga ɓangaren Sudan na fasalin yadda rundunar haɗin gwiwar za ta kasance, yana mai cewa wannan mataki ka iya kassara kyakyawar manufar da ake da ita na kiyaye zaman lafiya a Dafur. Rundunar ta haɗin gwiwa wadda zata ƙunshi dakarun soji 26,000 na Afirka da Majalisar ɗinkin duniya za su gudanar da aikin maido da tsaro da kwanciyar hankali ne a yankin wanda ya sha fama da rikici na tsawon shekaru huɗu. Nan da makwanni shida ake sa ran fara tura dakarun sojin.